001 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AZUMI

kashi na daya
TAQAITTACCEN BAYANI AKAN AZUMI DAGA LITTAFIN RISALA NA IBNU ABIY ZAIDEEN AL-QIRAWANIY
البيان موجز عن الصيام من كتب رسالة الإبن أبى زيد القيروانى
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاه والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Aslm
Ya! 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata, Manya Da Qanana, Da Fatan Muna Cikin Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu, Yayyunmu Da Qannanmu, Abokanmu Da Sa'o'inmu Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya, Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahman, In Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
-
A Gurguje
Insha Allahu Cikin Ikon Allah Ina Son In Dauko Mana Taqaitaccen Jawabin /raujimetawiy/ Akan Azumi, Daga Littafin Fiqhun Malikiyyan Nan, Wanda Aka Fi Sani Da #RISALA Na Abu Muhammad Abdullahi Binn Abiy Zaideen Al-Qirawaniy RH Babi Na Ashirin-Da-Uku, Da Yayi Masa Laqabi Da 
#Baabunn_Fis_Siyami.
-
Toh Amma Kafin Nan Ya Kamata Mu Kawo Aya 'Daya Zuwa Biyu Da Hadisi /raujimetawiy/ Dangane Da Wajabcin Azumi, Shin Azumin Da Mukeyi Mu Musulmai Al-Qur'ani Mai Girma Ya Umarce Mu Da Yi Ne? Ko Kuma Mu Muka Saka Kanmu Dayi?
-
Da Farko
قَالَ اللَّهُ تَعَالَى : يَأَيُّهَا الذِّينَ ءَامَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ كمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَقُونَ أَيَّامَّا مَعْدُودَاتِ.
ALLAH MADAUKAKIN SARKI YACE : Ya! Ku Wadanda Kukayi Imani ( Da Allah Shi Kadai Yake, Bashida Abokin Tarayya, Kuma Kukayi Imani Annabi Muhammad Manzon Allah Ne /raujimetawiy/ Kuma Bawansa ) An Wajabta Muku Yin Azumi, Kamar Yadda Aka Wajabta Akan Wadanda Suka Gabace Ku, ( A Ta Dalilin Yin Wannan Azumin ) Ko Kwa Zamo Masu Tsoro ( Taqawa, Tsoron Allah /raujimetawiy/ ) Ranaku/Kwanaki  Abin Qidanyawa/Lissafawa.
Suratul Baqarati.

Hakanan, ALLAH MADAUKAKIN SARKI Ya Sake Fada Mana Cikin Suratul Baqara
فَمَنْ شَهِيدَ مِنْكُمُ الشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ
Wanda Watan ( Azumin Ya Riske Shi /raujimetawiy/ Da Ransa Da Lafiyansa ) Toh Ya Azumce Shi.
.
Na Biyu Kuma
Idan Muka Koma Ga Hadisi Kuma Zamu Tarar Da Hadisi Kamar Haka.

قَالَ رسول الله صلى الله عليه وسلم : إِنَ اللَّهَ تَبَارَكَ وَتَعَالَى فَرَضَ صِيَامَ رَمَضَانَ عَلَيْكُمْ وَسَنَنْتُ لَكُمْ قِيَامُهُ فَمَنْ صَامَهُ وَقَامَهُ إِيمَانََا وَاحْتِسَابََا خَرَجَ مِنْ ذُنُوبِهِ كَيَومِ وَلَدَتْهُ أُمُهُ.
رواه أحمد وَالنَسائى
MANZON ALLAH S.A.W YACE : Lalle Allah Tabaraka Wata'alah Ya Farallanta/Wajabta Yin Azumin Watan Ramadan /raujimetawiy/ A Gareku, Ni Kuma Na Sunnata A Gareku Tsayuwansa ( Tsayuwan Dare Irinsu Sallahn Ashshan ETC ) Wanda /raujimetawiy/ Ya Azumce Sa, Ya Tsaya Masa Yana Mai Neman Lada, Zai Fita Daga Cikin Zunubansa Kamar Yadda Mahaifiyarsa/Uwarsa Ta Haifeshi.
Imamu Ahmad Da Nasa'i Ne Suka Rawaito.
-
Hakanan Idan Muka Je
SAHIHUL BUKHARI
2 KITABUL IMAN
1 BAABUNN IMAN, WA QAULUHU S.A.W BUNIYYAL ISLAM ALA KHAMSEEN
HADISI NA 8
MANZON ALLAH S.A.W YACE :
بُنِي الإسلام على خمس : شهادة أن لا إله إلا الله، وأن محمدا رسول الله، وإقام الصلاة، وإيتاء الزكاة، والحج، والصوم رمضان
An Gina Musulunci A Bisa Abubuwa
-
A Taqaice
Wannan Ya Ishemu Kafa Hujja Da Wajibcin Yin Azumin Watan Ramadan, /raujimetawiy/ A Duk Inda Muka Tsinci Mu Musulmai A Fadin Duniya.
Taa Duka-Duka Dai Cikin Ikon Allah Anan Zamu Tsaya, Don Saboda Kada Mu Tsawaita Rubutu, Insha Allahu Kuma A Kashi Na 002 Zamu Tashi Cikin Risalar Inda Malam Mai Littafi Allah Yayi Masa Rahma Yake Cewa : 
وصوم شهر رمضان فريضة يصام لرؤية الهلال ويفطر لرؤيته.

Abunda Muka Rubutu Dai-Dai Ubangiji Allah /raujimetawiy/ Ya Bamu Ladansa, Abunda Muka Rubuta Bisa Kuskure Ubangiji Allah Ya /raujimetawiy/ Yafe Mana Yayi Mana Gafara.
Ameen Summa Ameen
-
marubuci
@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, MVMech
-
12 Sha'aban 1446 Hijira
10 February 2025 Miladiyyah
Ranar Litinin
-
وداعا مع السلام

Comments

Popular posts from this blog

YAUSHE AKE SA RAI DA DAREN LAILATUL QADARI ETC

#64 HAPPY INDEPENDENCE DAY 2024