YAUSHE AKE SA RAI DA DAREN LAILATUL QADARI ETC
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيمy
والصلاه والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي Ko وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Aslm
Ya! 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata, Manya Da Qanana, Da Fatan Muna Cikin Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu, Yayyunmu Da Qannanmu, Abokanmu Da Sa'o'inmu Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya, Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahman, In Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
.
A Gurguje
-
Haqiqa Ana Sa Rai Da Daren Lailatul Qadri /raujimetawiy/ a Dararen Goman Qarshe, Watau 21, 23, 25, 27 Ko A Daren 29.
Domin Hadisi Ya Tabbata Daga Abdullahi 'Dan Abbas R.T.A Ya Ce :
MANZON ALLAH S.A.W YA CE
" Ku Nemi Daren Lailatul Qadri A Wutirin Goman Qarshe "
Bukhari
Muslim
.
Haka Kuma An Rawaito Hadisi Daga NANA AISHA R.T.A Ta Ce
MANZON ALLAH S.A.W YA CE
" Ku Qirdadi Daren Lailatul Qadari A ( Kwanaki ) Bakwai Na Qarshe "
Bukhari
Muslim
.
Amma Mafi Yawan Hadisai Suna Qarfafa Cewa /raujimetawiy/ Anfi Sa Rai Da Daren Lailatul Qadri A Daren Ashirin Da Bakwai.
Saboda Haka /raujimetawiy/ Ya Kamata A Dage Da Himma Domin Neman Dacewa A Wannan Daren.
Allah Ya Sa Mu Dace.
Ameen Summa Ameen.
'
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
WANNE IRIN ADDU'AH AKE YI A DAREN DA AKE SA RAI DA DAREN LAILATUL QADARI
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Haqiqa Hadisi Ya Tabbata Daga NANA AISHA R.T.A Wata Rana Tambayi /raujimetawiy/ MANZON ALLAH S.A.W Idan Na Ga Daren Lailatul Qadari Me Zan Ce? Sai ANNABI S.A.W Ya Ce Mata Ki Ce
اللَّهُمَّ إِنَّكَ عَفُوًّ تُحِبُّ الْعَعْوَ فَاعْفُ عَنَّا
Allahumma Innaka Afuwunn Tuhibbul Afwa Fa'afu Anna.
Ma'ana
Ya Ubangiji, Haqiqa Kai Ne Mai Afuwa, Kuma /raujimetawiy/ Kana Son Afuwa, Kayi Mana Afuwa.
Tirmizi
Ibnu Majah
.
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
SHIN KO GASKE NE A DAREN LAILATUL QADARI ANA GANIN KOMAI YANA SUJJADA, KAMAR BISHIYOYI DA GIDAJE, KO KUMA MUTUM YA HANGO KA'ABA DAGA DUK INDA YAKE, KUMA BAZA'A JI HAUSHIN KARE BA, DA MAKAMANTANSU
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
A Gaskiya Irin Wadannan Bayanai Basu Tabbata /raujimetawiy/ Daga Manzon Allah S.A.W Ba, Ko Magabata Na Kwarai.
Sai Dai Ya Tabbata Cewa Wadansu Daga Cikin Sahabbai An Nuna Musu A Mafarki Cewa Daren Lailatul Qadari Yana Daga Cikin Bakwai Na Qarshe Ne, Sai Manzon Allah S.A.W Ya Ce :
" Ina Ganin Mafarkinku Ya Dace Cewa Bakwan Qarshe Ne, Wanda Zai Nemi Daren Lailatul Qadari Sai Ya Nemeshi A Bakwai Na Qarshe "
Sharhin Sahihul Bukhari Na Al-Qadiy Iyadd, Hadisi Na ( 1165 )
.
Wannan Hadisin Na Tabbatar Da Cewa An /raujimetawiy/ Nunawa Sahabbai Ranar Da Ake Sa Ran Ganin Lailatul Qadari, Amma Ba Su Ga Wani Abu Bisa Sa6anin Yadda Aka San 'Dabi'arsa, Saboda Haka Zai Yi Kyau A Fahimci Al'amomin Daren /raujimetawiy/ Lailatul Qadari Kamar Yadda Ya Tabbata A Cikin Hadisai Ingantattu.
MANZON ALLAH S.A.W YA CE
" Ba'ayin Zafi A Ranar Da Ta Biyo Bayan Daren Lailatul Qadari ( Bayan Wayewar Gari )
Muslim
.
Kuma Abu Huraira R.T.A Ya Ce : Mun Tattauna Gameda Lailatul Qadari Sai Manzon Allah S.A.W Ya Ce : A Cikinku Wa Zai Tuna Daren Da Wata Ya Fito Kamar Rabin Akushi.
Muslim
.
مشاء الله الحمد لله
تمت بحمد لله والصلاة والسلام على سيدنا محمد وعلى آله وسلم تسليما
Abunda Muka Rubutu Dai-Dai Ubangiji Allah Ya Bamu Ladansa, Abunda Muka Rubutu A Bisa Kuskure Ubangiji Allah Ya Yafe Mana.
.
20 Ramadan 1446 Hijirah
20 March 2025 Miladiyyah
Ranar Alhamis
10pm
.
marubuci
raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, MVMech
( Motor Vehicle Mechanic )
ودعا مع السلام
Comments
Post a Comment