WADANNE HALAYE YA KAMATA MAI AZUMI YA SIFFANTU DA SU

@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاه والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Aslm
Ya! 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata, Manya Da Qanana, Da Fatan Muna Cikin Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu, Yayyunmu Da Qannanmu, Abokanmu Da Sa'o'inmu Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya, Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahman, In Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
-
A Gurguje
-
Ya Kamata Mai Azumi Ya Siffanta Da Kyawawan /raujimetawiy/ Halaye Kamar Haka:

01 - HAQURI : Ya Kamata Mai Azumi Ya Lazimci Haquri, Domin Shine Zai Hanashi /raujimetawiy/ Bin Son Zuciya.
Kuma Shine Zai Bada Juriyar Bin Umarnin Allah /raujimetawiy/
Hadisi Ya Tabbata Daga
MANZON ALLAH S.A.W CEWA
" Idan 'Dayanku Ya Kasance Yana Azumi, Kada Yayi Maganganun Fasiqanci, Idan Wani Ya Zageshi Ko Ya Yakeshi, Yace : Ni Azumi Nake Yi "
Bukhari
Muslim
-
02 - RIQON AMANA : Ya Kamata Mai Azumi Ya Kasance Mai Riqon Amana, /raujimetawiy/ Domin Riqon Amana Zai Taimaka Masa Wajen Bayar Da Haqqoqin Da Allah Ya Umarceshi Da Bayarwa. A Nan, Ya Zama Wajibi A Hankalin Wadansu Daga Cikin 'Yan Kasuwa Da Ke Amfani Da Watan Ramadan Wajen Cutar Da Al'umma Ta Hanyar Tsawwala Farashin Kayayyakin Masarufi, /raujimetawiy/ Da Kuma Yin Algus Ko Yaudara Da Rantse-Rantse Na Qarya A Cikin Ciniki.
Duk Abunda Aka Samu Ta Hanyar Haramun Toh Cinsu Ko Shansu Da Tufafinsu Ya Zama Haram.
Kuma /raujimetawiy/ Wannan Shine Abunda Zai Sa Allah Ya Qi Qar6an Adu'arsu, Haka Kuma Ana Qara Jawo Hankalin Shuwagabanni Wadanda Allah Ya 'Damqa Dukiyar Al'umma A Hannunsu Da Su Ji Tsoron Allah, Su Riqe Amana, Kada Su 'Debi Dukiyar Al'umma Su Tafi Dasu Umrah, /raujimetawiy/ Ko Su Biyawa Wadansu Mutane Don Biyan Buqatun Kansu, Ba Don Nufin Taimakon Al'ummarsu Ba.
Domin Allah Ba Ya Kar6an Ibadar Da Aka Yi Da Dukiyar Haram.
-
03 - RAHAMA/TAUSAYI : Ana Son Mai Azumi Ya Zama Mai Jin Qai, Da Yalwar Zuciya, Da Sakin Hannu Da Karamci, /raujimetawiy/ Kuma Mai Son Biyan Buqatan Al'umma Gwargwadon Hali. Domin
MANZON ALLAH S.A.W YA CE :
" Duk Wanda Ya Ciyar Da Mai Azumi, Yana Da Kwatankwacin Ladan Wanda Ya Ciyar, Ba Tareda An Rage Ladan Wanda Aka Ciyar 'Din Ba "
-
04 - NASIHA : Ya Kamata Mai Azumi Ya Zama Mai Nasiha Wajen Hana Mummunan /raujimetawiy/ Aiki, Da Kuma Umarni Da Kyakkyawar Aiki.
-
05 - SULHU : Ya Kamata Mai Azumi Ya Zama Mai Yin Sulhu A Tsakanin Mutane Da Ba Sa Jituwa, Musamman /raujimetawiy/ Idan Ya Shafi Dangi. Domin Ya Tabbata Cewa Qiyayya Tana Hana Kar6an Ibada Da Addu'ah, Har Sai Masu Adawar Sunyi Sulhu A Tsakaninsu.
-
06 - RINTSE IDO DA KAME FARJI : Ya Kamata Mai /raujimetawiy/ Azumi Ya Rintse Idonsa, Ya Kuma Kame Farjinsa Daga Dukkanin Abunda Allah Ya Hana, Musamman Kallon Mata Da Zina.
-
07 - KAME HARSHE : Ya Kamata Mai Azumi /raujimetawiy/ Ya Kame Harshensa Daga Giba ( Yi Da Mutane ) Da Zagin Mutane Da Cutar Da Su, Da Yarfe, Qazafi, Qage Da Qarya Ko Da Kuwa A Dandalin Siyasa Ne, Ko A Wajen Hira.
-
08 - IKHLASI : Ya Kamata Duk Mai Azumi Ya Qudurce Cewa Yanayin Azumin Ne Saboda Allah, Kuma Domin /raujimetawiy/ Neman Yardar Allah, Ba Don Mutane Su Yabe Shi Ba, Anan Ana Jan Hankalin 'Yan,uwa Masu Bada Sadaka Ko Ciyar Da Masu Azumi Da Masu Tafsirin Al-Qur'ani Mai Girma, Da Masu Zuwa Umrah, Da Limamai Masu Rera Tilawa A Sallar Tarawihi, Da Wasu Sauran Ayyuka Nagari Da Su Rinqa Yi Domin Neman /raujimetawiy/ Yardar Allah.
-
09 BIN SUNNAR MANZON ALLAH S.A.W : Ya Kamata Mai Azumi Yayi Koyi Da Sunnar Annabi S.A.W Sawu Da Qafa A Duk Ibadan Da Zaiyi. Ya Kuma /raujimetawiy/ Nisanci Dukkan Bidi'o'i, Musamman Ma Bidi'o'in Da Ake Yinsu A Cikin Watan Ramadan, Kamar Yin Sallan Nafila Wanda Basuda Asali Daga Manzon Allah S.A.W, Ko Magabata Na Kwarai, /raujimetawiy/ Kamar Nafilar Da Akeyi Kowanne Dare Bayan Sallar Asham, Kowanne Dare Da Adadin Raka'o'insa Da Ladan Da Aka Qago Aka Jinginawa Manzon Allah S.A.W /raujimetawiy/
-
10 - TARBIYYAH : Ya Kamata Mai Azumi Ya Kula Da Tarbiyyar Gidansa, Musamman Kangararrun Yara /raujimetawiy/ Wadanda Suke Sakaci Da Sallah Da Azumi, Ko Kuma Shaye-Shaye. Kuma Ya Kamata Iyaye Su Yawaita Yiwa 'Ya'yansu Adu'ah A Cikin Watan Azumi, Domin Allah Ya Shiryesu, Kuma Muna Jawo Hankalin Iyayen Da Ke Sanya Fina-finai, Musamman A Cikin /raujimetawiy/ Ramadan Da Sunan Rage Dare Ko Rana, Da Su Ji Tsoron Allah Kuma Su Nisanci Wannan Mummunar 'Dabi'ar.
-
Masha Allah Alhamdulillahi
Tamatt Bi Hamdi Lah, Wa Sallallahu Ala Nabiyy Kareem.
.
Abunda Muka Rubutu Dai-Dai Ubangiji Allah Ya Bamu Ladansa, Abunda Muka Rubutu A Bisa Kuskure Ubangiji Allah Ya Yafe Mana.
.
17 Ramadan 1446 Hijirah
17 March 2025 Miladiyyah
Ranar : Litinin
1pm
.
marubuci
#raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, MVMech

Comments

Popular posts from this blog

YAUSHE AKE SA RAI DA DAREN LAILATUL QADARI ETC

#64 HAPPY INDEPENDENCE DAY 2024

RABIU ALHAJI UMAR JIMETAWIY PERSONAL INFORMATION