TAQAITACCEN BAYANI AKAN YA YA AKE YIN SALLAN IDI
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبى وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل البيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
السلام عليكم ورحمة الله تعالى وبركاته
يا إخواني المسلمين نساء ورجالا صفيرا وكبيرا أرجو نحن بخير والعافية، نسأل الله سبحانه وتعالى أن يقبل صيامنا، رب شفي كل مرضانا، ويغفر ويرحم كل أمواتنا الذين سبقونا بموت، أمين يا رب
Aslm
Ya ‘Yan,uwana Musulmai Msza Da Mata Manya Da Qanana Ina Fata Muna Cikin Qoshin Lafiya, Kuma Muna Roqon Allah Ya Karɓa Mana /raujimetawiy/ Azuminmu, Ya Kuma Yaye Wa Marasa Lafiyanmu, Ya Yi Rahma Da Jin Qai Ga Dukkan Mamatanmu Da Suka Riqamu Mutuwa. Allahumma Ameen Ya Rabbil Alaamin.
.
بإذن الله تعالى اليوم أريد أن أكتب شيئا عن الصلاة العيد وكيف يفعلها
A Yau Da Izinin Allah Nake Qudirin Rubuta Wani Abu /raujimetawiy/ Akan Sallan Idi Da Kuma, Yaya Akeyinta.
.
كلنا أو أقول جلنا عرفنا كيف يفعلها، إلا أن أجددنا
Dukanmu Dai Ko Ince Mafi Yawancinmu Munsan Yaye Akeyin Sallan Idi, Sai Dai Kawai Dai In Qara Mana Tishi.
RabiuAlhajiUmarJimetawiyPAN
.
سأكتب هذا البيان من كتاب الشيخ أبى الحسن علي المالكي الشاذلى رحمه الله تعالى، المقدمة العزية
Sai Dai Shi Wannan Bayanin Zan Rubuto Shine Daga Littafin Sheikh Abi Hassan Aliyu Al-malikiy Ash-shaziliy Allah Ya Yi Masa Rahma, Wato littafin Iziyyah, Wanda / raujimetawiy/ Qaramin Littafi Ne Na Fiqhun Malikiyyah, Wanda ‘Daliban Fiqhu Suke Yawan Kuka Da Littafin Saboda /raujimetawiy/ Wahalansa.
.
فقد كتب مصنف فى كتابه باب الثانى فصل عشرون،
Haqiqa Mallam Mai Littafi a Rubuta Wannan Bayanin A Littafinsa, A Babi Na Biyu, Fasali Na Ashirin.
.
وقال الشيخ
صلاة العيدين (عيد الفطر و الأضحى، وهو مراد بعيدين) وهي سنة مؤكدة فى حق من تلزمه الجمعة.
Wa Qala Sheikh
Wato Ita Sallan idi Biyu ( In Ance Sallan Idi Biyu, /raujimetawiy/ Ana Nufin Sallan Azumi Da Na Layya) Ita Sunnah Ce Mai Qarfi Akan Wanda Sallan Juma’ah Ta Lazimta Akansa.
.
مستحبة فى حق العبد والمسافر والمرأة ( يستحب لهم أن يحضروها)
Anso A Cikin Haqqin Bawa Da Matafiyi Da Mace (Wato Anso Su Halarceta)
.
وصفتها ركعتان، بغير أذان ولا إقامة
Suffar Ita Sallan Idin Raka’ah Biyu Ce, Amma /raujimetawiy/ Ita Kuma Ba’a Yi Mata Qiran Sallah Ko Tayar Da Iqama.
كما جاء فى الموطأ المالك
كتاب العيدين
باب العمل فى غسل العيدين والنداء فيهما والإقامة
حديث ٤٣١
حدثنى يحيى عن مالك أنه سمع غير واحد من علمائهم يقول : لم يكن فى عيد الفطر ولا فى الأضحى نداء ولا إقامة منذ زمان رسول الله صلى الله عليه وسلم إلى اليوم.
قال مالك وتلك السنة التى لا اختلاف فيها عندنا.
Kamar Dai Yadda Ya Zo A Muwadda Malik
Kitabul Idaini
Babin Aiki Cikin Wanka Idi Biyu Da Yin Qiran Sallah Da Yin Iqama Acikinsu
Hadisi Na 431
Haddasani Yahya Ann Malik, Shi imam Malik Yaji Daga Wani Wanda Ba ‘Daya Bane Daga Cikin Malamansu Yana Cewa : lalle Shi Yin Qiran Sallan Ko Tada iqama Bai Kasance /raujimetawiy/ Anayinsa Ba Tun Zamanin Manzan Allah sS.A.W Har Izuwa Yau.
Imam Malik Yace Lalle Wannan Sunnar Wacce /raujimetawiy/ Babu Saɓani A Cikinta Haka Al,amarin Yake A Gurinmu, Babu Saɓani.
.
يكبر فى (ركعة) الأولى بعد تكبيرة الإحرام ست تكبيرات، وفى (ركعة الثانى) خمس تكبيرات بعد تكبيرة القيام.
Ana Yin Kabbarori Guda Shida Banda Ta Kabbarar Harama, A Raka’ar Farko, A Raka’ah Ta Biyu Kuma Bayan Anyi Kabbarar Tsayuwa, Shi Kuma Kabbara Biyar Akeyi.
كما جاء فى الموطأ المالك أيضا
كتاب العيدين
باب فى التكبير والقراءة فى صلاة العيدين
حديث ٤٣٩
حدثنى عن مالك عن نافع مولى عبدالله بن عمر إنه قال : شهدت (صلاة) الأضحى والفطر مع أبى هريرة فكبر فى الركعة الأولى سبع تكبيرات قبل القراءة، وفى الآخرة خمس تكبيرات قبل القراءة.
Kamar Dai Yadda Ya Sake Zuwa A Muwadda Malik Kuma
Kitabul Idaini
Babin Da Yake Magana Akan Kabbarori Da Ake Yi Da Sallan Karatun Da Ake Yi A Sallan Idi
Hadisi Na 439
Haddasani Ann Malik Ann Nafi’in Maula Abdullahi ‘Dan Umar Shi Yace : Na Halarci ( Sallan Idi ) Na Layya Da Na Azumi, Tare Da Abi Huraira, Sai Aba Huraira Yayi Kabbarori Guda Bakwai A Raka’ar Farko Kafin Fara Karatu, A ‘Dayan Raka’ar Kuma Sai Yayi Kabbara Guda Biyar Kafin Fara Karatu.
RabiuAlhajiUmarJimetawiy
.
ولا يستحب رفع اليدين فى شيء من (سائر) التكبير سوى تكبيرة الإحرام.
Ba’aso ‘Daga Hannaye A Cikin Sauran Kabbarori Ba, Amma Ta Farko/Ta Harama Za’a ‘Daga Hannu.
..
وإن نسي (إمام) التكبير (من تكبيراتها) رجع إليه ما لم يضع يديه على ركبتيه ، وسجد بعد السلام
Idan (liman) Ya Manta Yin Wata Kabbara ( Daga Cikin Kabarorinta ) Toh Sai Ya Dawo Izuwa Gareshi Wato Yayi Kabbaran, Amma /raujimetawiy/ Muddin Bai ‘Dora Hannayensa Akan Gwuwwowinsa Wato Ruku’u Kenan, Idan Ya Idar Sai Yayi Sujjadar Ba’adi.
.
ويستحب الجهر بالتكبير ، والتطيب والتزين بالثياب الجديدة لمن يقدر عليها
Hakan Kuma Anso Bayyana Yin Kabbarorin A Sarari/Fili, Anso Shafa Turare Da Sanya Tufafi Sabo Amma Ga Wanda Yake Da Ikon Yin Hakan/’Dinkawan.
.
والرجوع من طريق غير التى جاء منها
Da Dawowa Daga Masallacin Idi Ta Hanyar Wacce Ba Ta Ita Ka Je Ba.
Domin Hadisi Yazo A Sahihul Bukhari, Manzon Allah S.A.W Ya Kasance, /raujimetawiy/ Idan Ranar Idi Ta Kasance, Yana Sa6a Hanya.
Ga Hadisin Nan Kamar Haka
صحيح البخاري
١٩ - كتاب العيدين
٢٤ - باب: من خالف الطريق إذا رجع يوم العيد.
٩٤٣ - حدثنا محمد قال: أخبرنا أبو تميلة، يحيى بن واضح، عن فليح بن سليمان، عن سعيد بن الحارث، عن جابر قال:
كان النبي صلى الله عليه وسلم، إذا كان يوم عيد، خالف الطريق.
تابعه يونس بن محمد، عن فليح، عن سعيد، عن أبي هريرة، وحديث جابر أصح..
.
والفطر (تأكل الطعام قبل ذهاب إلى المصلى) قبل الرواح إلى المصلى فى عيد الفطر، وتأخيره (ترك تأكل الطعام) فى عيد النحر.
Hakanan Da Yin Fiɗiri ( Wato Cin Abinci ) Kafin A Tafi Izuwa Sallan Idi, Amma Kuma A Sallar Layya Kuma Sai A Jinkirta/Barin Cin Abincin Har Sai An Dawo Daga Idin.
.
كما جاء فى الموطأ المالك أيضاً
كتاب العيدين
باب الأمر بالأكل قبل الغدو فى العيد
حديث ٤٣٦
Kamar Yadda A Qara Zuwa A Muwadda Malik Kuma
Kitabul Idaini
Babin Umarni Da Cin Aɓinci Kafin Tafiya Zuwa Sallan Idi
Hadisi Na 436
حدثنى يحيى عن مالك عن هشام بن عروة عن أبيه أنه كان يأكل يوم عيد الفطر قبل أن يغدو
Haddasani Yahya Ann Malik Ann Hishamm Bin Urwa Daga Babansa Shi Baban Nasa Ya Kasance Yana Cin Abinci A Sallan Azumi Kafin Ya Tafi Izuwa Gurin Sallan Idi.
/raujimetawiy/
.
مشاء الله الحمد الله
سأوقف هنا بإذن الله تعالى، فقد عرفت طولت بيان، ولذلك أقول من فضلكم اجعلونى من دعائكم ولا تنسى بى فى دعائكم، اليوم نحن فى ليلة تسع وعشرون، أرزقنا الله بليلة القدر. أمين
Masha Allah Alhamdulillahi
Da Izinin Allah Zan Tsaya Anan, Domin Ni Kaina Nasan Na Tsawaita Bayani, Da Wannan /raujimetawiy/ Nake Cewa Dan Allah Ku Sanyani Cikin Adu’o’inku Karku Manta Da Ni, Yau Dai Muna Cikin Daren Ashirin Da Tara, Allah Ya Azurtamu Da Daren Lailatul Qadri. Ameen
.
٢٨ رمضان ١٤٤١ هجرية
٢١ مايو ٢٠٢٠ ميلادية
يوم الخميس
٠٨م – ١٠م
28 Ramadan 1441 hijriyya
21 May 2020 miladiyyah
Ranar Alhamis
08pm – 10pm
.
@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, PAN
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@ @@
وزيادة عن ذالك
QARI AKAN HAKA
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@ @@
وأما فى عيد الأضحى هناك أذكار الذى يفعل فى يوم الأضحى وثلاث أيام الذى يليه
Amma A Idin Layya, Akwai Azkarai Da Ake Yi A Ranar Layya Da Kwana Uku Da Yake Bin Ranar Idin.
.
وقال الشيخ رحمه تعالى فى آخر هذا باب
Mallam Allah Ya Yi Masa Rahma Yace A Qarshen Wannan Babin.
.
والتكبير فيه عقب خمس عشرة (الصلاة) فريضة
Da Yin Kabbarori Bayan ( Salloli ) Farillah Guda Goma Sha Biyar,
.
أولها ظهر يوم النحر ( يبدأ يوم النحر بعد فرغ الصلاة الظهر)
Farkonta
Ana Fara Wannan Zikirin Bayan An Idar Da Sallar Azahar Ranar Layya.
وآخرها صبح اليوم الرابع منه
Ana Qare Wannan Zikirin A Rana Ta Huđu A Sallar Asuba.
وصفة التكبير
Siffar Yadda Ake Yin Kabbarar
Shine Kamar Haka
الله أكبر الله أكبر الله أكبر لا إله إلا الله والله أكبر الله أكبر ولله الحمد
Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar, La,ilaha illallah, Wallahu Akbar, Allahu Akbar, Walillahi Hamdu.
.
٩ ذو الحجة ١٤٤١ ھ
٣٠ يوليو ٢٠٢٠ م
يوم الخميس
9 Zul-Hijjah 1441 h
30 July 2020 m
ranar Alhamis.
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Wannan Rubutu Nayi Shi Shekaru Biya Baya, Amma Kuma Yanzu Nayi Tahdidinsa/Editing Na Shi, Domin Gyara Wasu Kura-Kuran.
raujimetawiy
Abunda Muka Rubuta Dai-Dai Ubangiji Allah /raujimetawiy/ Ya Bamu Ladansa, Abunda Muka Rubuta A Bisa Kuskure Kuma Ubangiji Allah Ya Gafarta Mana.
Ameen Summa Ameen
.
29 Ramadan 1446 Hijrah
29 March 2025 Miladiyyah
Ranar Juma’ah
5am
.
raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, MVMech
( Motor Vehicle Mechanic )
وداعا مع السلام
https://raujimetawiy.wordpress.com/2024/06/14/taqaitaccen-bayani-akan-ya-ya-ake-yin-sallan-idi/
Comments
Post a Comment