TAQAITACCEN BAYANI AKAN ZAKKAN FIDDA KAI
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاه والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Aslm
Ya! 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata, Manya Da Qanana, Da Fatan Muna Cikin Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu, Yayyunmu Da Qannanmu, Abokanmu Da Sa'o'inmu Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya, Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahman, In Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
.
A Gurguje
.
Yau Insha Allahu Zamu 'Dauko Taqaitaccen /raujimetawiy/ Bayani Akan Zakkatul Fidiri, Wanda Malam Bahaushe Yake Cewa Zakkan Fidda Kai.
Insha Allahu Zamu 'Dauko Wannan Jawabin /raujimetawiy/ Daga Littafin RISALA Na IBNU ABIY ZAIDEEN AL-QIRAWANIY RH
.
Amma Kafin Farawa Akwai Buqatan Yin Qarin Bayani Akwai, Da Kuma Bayanin Mene Ne /raujimetawiy/ H Hikiman Yinsa, Banida Lokacin Yin Haka A Halin Yanzu, Amma Kuma Tuntu6i Malaman Sunnah ( Masu Karantar Da Addinin Musulunci, Ba Malaman Tsubbu Ba )
Ko Kuma Juma'ah Nan Mai Zuwa ( 28 Ramadan 1446 / 28 Mar 2025 ) Je Ka Sallan Juma'ah Da Wuri, Zakaji /raujimetawiy/ Qarin Bayani Daga Bakin Masu Abun.
.
A Gurguje, Cikin Littafi
RISALA
BABI NA 27
BABUN FI ZAKKATIL FIDRI
وَزَكَةُ الْفِطْرِ سُنَّةُ وَاجِبَةً فَرَضَهَا رَسُوْلُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلّمَ
Shi Zakkatul Fidiri ( Zakkan Fidda Kai ) Sunnah Ce /raujimetawiy/ Wajiba, Manzon Allah S.A.W Ne Ya Farillanta Ta.
عَلَى كُلِّ كَبِيرٍ أَوْ صَغِيرٍ، ذَكَرٍ أَوْ أُنْثَى، حُرٍّ أَوْ عَبْدٍ مِنَ الْمُسْلِمِينَ
A Bisa Ga Dukkan ( Mutum ) Musulmi Babba Ko Qarami, Mace Ko Namiji /raujimetawiy/ 'Da Ko Bawa.
صَاعًا عَنْ كُلِ نٓفْسٍ بِصَاعٍ النَّبِيِّ ص:
Sa'i Guda 'Daya, Ga Kowanne Rai ( Mutum ) /raujimetawiy/ Sa'in Kuma, Irin Sa'in Annabi S.A.W
وَتُؤَدَّى منْ جُلِّ عَيْشِ أَهْلُ ذَلِكَ الْبَلَدِ
Ana Bayarwa Ne Daga Mafi Rinjaye Abunda Mutanen /raujimetawiy/ Wannan Gari Suke Ci,
مِنْ بُرِّ
Daga Alkama
( Inya /raujimetawiy/ Kasance Mutanen Garin Shi Suke Ci )
أَوْ شَعِيرٍ
Ko Sha'ir
أوْ سُلْتِ
Ko Acca
أَوْ تَمرٍ
Ko Dabino/Dibino
أَوْ أُقِطٍ
Ko Cukwai
أَوْ زَبِيبٍ
Ko Zabibi
أَوْ دُخْنٍ
Ko Gero
أَوْ ذُرَةٍ
Ko Dawa
أَوْ أُرْزِ
Ko Shinkafa,
وَقِيلَ : إِنْ كَانَ العَلَسُ قُوتَ أُخْرِجَتْ مِنْهُ
Wa Qila Ance : Idan Ya Sa Kasance Alass Ne, Mafi Rinjayen Abunda Ake Ci ( A Wannan Garin ) Toh Sai Fitar ( Da Zakkan ) Daga Alass In,
وَهْوَ حَبٌّ صَغِيرٌ يَقْرُبُ مِنْ خِلْقَةِ الْبُِرِّ
Wa Huha, Shi ( Alass In ) Yana Nan Kwaya Ne Qanana, Kamaninsa Yayi Kusa Da /raujimetawiy/ Kamannin Alkama.
.
Domin Tabbar Da /raujimetawiy/ Matanin Wannan Maganar, Je Kai
MUWADDA MALIK
17 KITABUL ZAKKATI
28 BABUN MAKILATI ZAKKATIL FIDRI
HADISI NA 629
حَدَّثَنِي يَحْيَى عَنْ مَالِكٍ عَنْ نَافِعٍ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَرَضَ زَكَاةَ الْفِطْرِ مِنْ رَمَضَانَ عَلَى النَّاسِ صَاعًا مِنْ تَمْرٍ أَوْ صَاعًا مِنْ شَعِيرٍ عَلَى كُلِّ حُرٍّ أَوْ عَبْدٍ ذَكَرٍ أَوْ أُنْثَى مِنَ الْمُسْلِمِينَ.
Yahaya Ya Fada/Gaya Mini, Daga Malik, Daga Nafi'in, Daga Abdullahi 'Dan Umar, Lalle Manzon Allah S.A.W Ya Wajabta Zakkan Fidda Kai Ga Mutane, Bayan Ramadana, Sa'i 'Daya Daga Dabino, Ko Sa'i Daga Sha'ir, ( An Wajabta Shi ) A Bisa Ga Dukkan Musulmi 'Yantacce Ko Bawa, Mace Ko Namiji.
.
وَيُخْرَجُ عَنِ الْعَبْدِ سَيِّدُهُ
Bawa Shugabansa ( Wanda Yake Shugabantansa ) Shi Zai Fitar Masa Da /raujimetawiy/ Zakkan Fidda,
Kansa
وَالصَّغِيرُ لاَ مَالَ لَهُ يُخْرِجُ عَنْهُ وَالِدُهُ
Hakanan Yaro Qarami Wanda Bashida Kudi, Mahaifinsa Sai Ya Fitar Masa ( Allah Ya Qara Buda Mana, /raujimetawiy/ Mu Fitarwa Kanmu, Mu Fitarwa Iyayenmu, Ameen )
وَيُخْرِجُ الرَّجُلُ زَكَاةَ الْفِطْرِ عَنْ كُلِّ مُسْلِمِ تَلْزَمُهُ نَفَقَتُهُ
Hakanan Mutum Namiji Zai Fitarwa Dukkan /raujimetawiy/ Musulmin Da Ciyar Dashi Ya Lazimce Shi,
وَعَنْ مُكَاتَبِهِ وَإِن كَانَ لاَ يُنْفِقً عَلَيْهِ لِأَنَّهُ عَبْدً لهُ بَعْدُ
Hakanan Bawa Makatib ( Wato Bawa Wanda Aka Rubutawa Masa Adadin Kudin Da Inya Biya Zai Zama 'Yantacce, Toh /raujimetawiy/ Shugabansa Zai Fitar Masa Da Zakkan Fiddan Kai ) Ko Da Ya Kasance Baya Ciyar Dashi, Saboda Dukda /raujimetawiy/ Haka Bawansa Ne.
.
وَيُسْتَحَبُ إِخْرَجُهَا إِذَا طَلَعَ الْفَجرِ مِنْ يَومِ الْفَجْرِ،
An So Fitar Da ( Zakkan Fidda Kai ) Idan Alfijir Ya Fito A Ranar Sallan Azumin ( Qaramin Sallah , Astagfirullah )
( Amma Abu Hassan Aliyu Al-Malikiy Ash-Shazaliy RH Cikin Littafinsa Mai Suna MUQADDIMATUL IZIYYAH
Ya Ce :
وَيَجُوزُ إِخْرَاجُهَا قَبْلَ يَوْمِ الْعِيدِ بِالْيَوْمَيْنِ وَالثَّلاَثَة
Ana Yuwa A Fitar Da Zakkan Fidda Kai, Tun Sallah Saura Kwana Biyu Ko Uku. )
وَيُسْتَحَبُ الفِطْرِ فِيْهِ قَبْلَ الْغُدُوِ إِلَى المُصَّلِى وَلَيْسَ ذَلِكَ فِى الأُضْحَى
( A Sallan Azumin ) An So Cin Abinci ( A Ci Abinci ) Kafin A Tafi Wajen /raujimetawiy/ Sallan Idi,
Amma Kuma A Sallan Layya Kuma Anfi So Sai An Dawo Daga Idi,
وَيُسْتَحَبُ فِى العِيدَينِ أَن يَمْضِي مِنْ طَرٓيقٍ وٕيَرْجعُ مِنْ أُخْرَى
An So A Cikin Idi Biyu ( Sallan Azumi Da Sallan Layya ) Mutum In Zai Je ( Sallan Idi ) Ya Je Ta Wata Hanya Dabam, Ya Dawo Ta Wata Hanya Dabam.
Hadisi Ya Zo Akan Hakan, Amma Amini Uzuri Yanzu, Bazan Samu Daman Kawo Hadisin Ba, Sbd Matsalar Rashin Tsayuwan Wutan Lantarki, /raujimetawiy/ Bani Da Isheshshen Caji,
Amma A Rubutu Na Mai Taken
YAYA AKE SALLAN IDI
Ina Kyautata Zaton Na Rubuta Hadisin, Insha Allahu Posting Na Gaba, Zan Kawo Shi.
.
تمت بحمد لله وحسن عونه
وصلى الله على نبي الكريم
Wannan Shine Qarshe Wannan Fasali,
Abunda Muka Rubutu Dai-Dai Ubangiji Allah Ya Bamu Ladansa, Abunda /raujimetawiy/ Muka Rubuta A Bisa Kuskure Ubangiji Allah Ya Yafe Mana Yayi Mana Gafara.
.
26 Ramadan 1446 Hijirah
26 March 2025 Miladiyyah
Ranar : Laraba
2pm
.
marubuci
#raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, MVMech
( Motor Vehicle Mechanic )
وداعا مع السلام
.
Comments
Post a Comment